SOJOJIN NAJERIYA SUN YI IKIRARIN SAKE KWATO GUDUMBALI
Rundunar sojin Najeriya ta
sanar da sake kwato garin Gudumbali daga hannun Boko Haram, bayan da mayakan
rahotanni suka ce mayakan sun mamaye wanan gari da ke jihar Borno a ranar
asabar da ta gabata.
Kakakin rundunar tsaron
Najeriya Burgediya Janar Texas Chukwu, wanda a jiya asabar ya ce ba ya da
masaniya game da labarin da ke cewa ‘yan Boko Haram sun kwace garin, a wannan
lahadi ya ce ‘’tabbas an yi wani artabu a yankin tare da kona gidaje da dama,
amma daga bisani maharan sun janye’’.
Janar Chukwu ya ce ba a samu
asarar rayuka ba, sannan kawo yanzu an dawo da doka da oda tare da tura
karin sojoji zuwa yankin’’ a cewarsa.
A ranar asabar da ta gabata
ne bayanai suka nuna cewa wani adadi mai tarin yawa na ‘yan Boko Haram ya kwace
ikon garin na Gudumbali bayan da suka fatattaki sojojin da ke cikin wani bariki
a yankin.
Har ila yau bayanan farko sun
ce an kashe fararen hula akalla 8 lokacin wannan artabu.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku