KUNGIYOYI HUDU SUN SIYA WA EL-RUFAI FOM DIN TAKARA
Kungiyar Dillalan Man Fetur, IPMAN, Kungiyar
Direbobin Tankunan Mai, PTD, Kungiyar Direbobin Motocin Haya, NARTO, Kungiyar
‘Yan kasuwan Sheikh Mahmood Gumi dake Kaduna da Kungiyar Katsinawa da Daurawa
mazauna Kaduna ne suka yi karo-karo suka siya wa gwamnan jihar Kaduna Nasir
El-Rufai fom din takarar ta zarce.
Jagoran gamayyar kungiyoyin Abbas Likoro ya bayyana
cewa sun yi wa gwamna El-Rufai goma ta Alheri ne ganin yadda ya jajirce wajen
yin aiki tukuru a jihar Kaduna.
” Dukkan mu mun
gamsu da irin ayyukan ci gaba da gwamna El-Rufai ya ke yi a jihar Kaduna.
Mambobin kungiyoyin
sun ya tattaki na musamman zuwa fadar gwamnati domin mika wa gwamna El-Rufai
fom din.
A fadar gwamnati
El-Rufai ya gode musu matuka inda ya ce dama can da tunanin inda zai sami kudin
siyan fom din yake kwana ya da ita yaketashi.
” Tun da jam’iyya
ta sanar da kudin fom din na fada cikin damuwa domin kuwa bani da irin wadanna
kudi a asusun ajiya na banki.
” Shi kan sa
shugaban kasa Muhammadu Buhari da yaji kudin sai da ya koka ya ce ba ya da
wannan kudi. Bayan mun tafi kasar Chana sai mu ka yanke shawarar zamu yi
karo-karo na naira Miliyan bibbiyu daga kowani gwamna domin siya masa fom din.
” Kwatsam sai muka
ji wai wata kungiya ta siya masa fom din. Da na gaya masa sai ya tambayeni cewa
ni kuma wa zai siya min.
El-Rufai ya gode wa
wadannan kungiyoyi da suka yi masa wannan namijin kokari sannan suka fitar da
shi kunya tun da bashi da kudin siyan fom din dama.
Ya shaida musu cewa
gwamnatin sa za ta ci gaba da yi wa mutane ayyukan ci gaba kamar yadda ta yi
alkawari.
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku