WHO ZA TA BADA GUDUNMAWAR MAGANIN RIGAKAFIN ZAZZABIN SHAWARA A NAJERIYA
Jami’ar
kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) Charity Warigon ta bayyana cewa kungiyar
WHO za ta ba Najeriya gudunmawar maganin allurar rigakafi zazzabin shawara har
na miliyan 12 a shekarar 2018 sannan ta kara bada magani na miliyan 19 a 2019.
Charity ta bayyana haka ne a Abuja inda ta kara da cewa WHO za
ta samar da wannan gudunmawa ne da hadin guiwar Kamfanin GAVI.
A wani rahoton hukumar kula da hana yaduwar cututtuka ta
Najeriya (NCDC) zazzabin shawara ta bullo a kananan hukumomi 22 a kasar nan,
sannan mutane 4200 sun kamu kuma 47 sun rasu cikin su.
Charity ta ce suna kokarin ganin an kau da wannan zazzabi zuwa
2026.
Za a far yin allurar ne daga ra 8 zuwa 18 ga watan Nuwamba, a
jihohin Sokoto, Kebbi, Neja, Filato, Barno da babban birnin tarayya Abuja.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html

Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku