WASANNI : ZAI YI WAHALA MANCHESTER UNITED TA YI ABIN KIRKI A BANA – INJI SCHOLES
Magoya bayan Manchester United tare da wasu tsaffin ‘yan wasan kungiyar, suna ci gaba da bayyana rashin kwarin giwar da suke da shi, dangane da samun nasarar United din a kakar wasa ta bana.
Tsohon dan wasan
kungiyar na baya bayan nan da yayi tsokaci kan halin da kungiyar ke ciki shi ne
Paul
Scholes, wanda ya ce
ba shakka rashin sayen manyan ‘yan wasa sai sa United fuskantar matukar wahala
a kokarin ta na lashe kofuna a bana musamman ma na Premier.
Ko a makon daya
gabata ma dai kocin kungiyar Jose Mourinho ya koka bisa yadda basu samu nasarra
sayen manyan ‘yan wasa ba a kasuwar da aka kare ci, baya ga mai tsaron raga Lee
Grant, dan tsakiya Fred da kuma Diogo Dalot.
A makon da ya gabata,
dan wasan gaba na Manchester United Alexis Sanchez ya ce tilas kungiyar tasa ta
sayo ‘yan wasa kwatankwacin Arturo Vidal da kungiyar Barcelona ta saya a baya
bayan nan, idan har tana son lashe kofuna a kakar wasa ta bana.
Sanchez ya bayyana
bukatar ce a dai dai lokacin da ake shirin rufe kasuwar cinikin ‘yan wasa,
bayan da mai horar da United Jose Mourinho ya bayyana fatan ‘yan wasa biyu daga
kungiyoyin Leicester da Bayern Munich, wato Harry Maguire da Jerome Baoteng.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku