SHUGABAN MAJALISAR DINKIN DUNIYA YA NADA AMAECHI BABBAN MUKAMI


Majalisar dinkin Duniya ta sanar da wani muhimmin nadi da ta yi ma tsohon gwamnan jihar Ribas, kuma ministan sufurin Najeriya, Chibuike Rotimi Amaechi, wanda ta nada shi mamba a kwamitin gudanarwa na gidauniyar kiyaye haddura akan tituna na Duniya.
Jaridar Africanjournalist.info ce ta bayyana haka a shafinta, inda tace majalisar ta sanar da nadin Amaechi ne a Geneva, kasar Switzerland, wanda a yanzu haka ministan yana can kasar, inda yake wakiltar Najeriya a taron gidauniyar dake gudana.
Majalisar ta nada Amaechi ne domin ya kirkiro hanyoyin rage aukuwar haddura, rage adadin mutanen da hatsari ke rutsawa dasu tare da tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin mutane akan hayoyin Duniya gaba daya.
Wata majiya a Najeriya ta ruwaito haidimin Ministan akan kafafen watsa laabru, Israel Ibeleme yace tattaunarwa da ake gudanarwa a yanzu haka a Geneva, da kuma shawarwarin da za’a yanke a can, zasu taimaka matuka wajen ganin gidauniyar ta amfani al’ummar Duniya.

DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/

ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html

Comments