SANATOCI 49 SUN NUNA ADAWA DA YUNKURIN TSIGE SARAKI DA EKWEREMADU


Akalla sanatoci 49 na tarayyar Najeriya ne suka nuna adawarsu da yunkurin tsige shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da mataimakinsa Farfesa Ike Ekweremadu.



Ku tuna cewa tun a asubahin yau ne jami’an DSS suka mamaye majalisar dokokin Najeriya sannan suka hana mutane shiga harabar majalisar. Haka zalika jami’an tsaron sun hana yan majalisa da dama, musamman masu biyayya ga Saraki da Ekweremadu shiga majalisar yayinda suka bar yan APC suka shiga.

Sanatan dake wakiltan Bayelsa ta gabas Ben Murray-Bruce yayinda ya jagoranci sauran yan majalisa wajen adawa da mamayar, yace sanatocin APC ne suka shirya hakan sannan kuma cewa suna shirin tsige Saraki da Ekweremadu sannan su daura sanata Godswill Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa.

Yace wannan makirci da sanatocin APC ke shiryawa ba zai yi nasara ba domin jam’iyyar PDP ce ke da masu rinjaye a majalisar dattawa.



DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/

ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html

Comments