MUTUMIN DA DAN SA YA RASU SANADIYYAR AZABTARWAR SARS YA NEMI HAKKIN SA
Wani mutum mai suna Hassan Abdullahi,
ya nemi rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bi umarnin kotu ta hanyar biyan diyyar
naira miliyan 10 da kotu ta umarci ‘yan sanda su biya, sanadiyyar mutuwar da
dan sa ya yi a hannun jami’an SARS, saboda azabtarwa.
Abdullahi
ya shaida wa Sashen Hausa na BBC a yau Labara, yadda dan karamin rashin jituwa
tsakanin Hassan da ‘yar uwar sa ya kai su ofishin ‘yan sanda a Kano.
Abdullahi
ya yi ikirarin cewa yayin da aka je ofishin ‘yan sanda, sai SARS suka maida
rashin jituwar zuwa zargin fashi da makami, daga nan suka rika gallaza wa
Hassan har hakan ya yi sanadiyyar mutuwar sa.
A
hirar da aka yi tsakanin Abdullahi da wakilin BBC, ya ce sabani aka samu
tsakanin Hassan da ‘yar uwar sa, daga nan sai ta kai shi kara ofishin ‘yan
sanda.
“Amma
a ofishin ‘yan sanda, sai suka ce min wai ‘yan fashi da makami ne, kuma aka
dauke su zuwa ofishin SARS, inda dan nawa Hassan ya sha azaba a hannun su.
“A
wannan daren sai SARS suka kira ni, suka ce min wai da na ya na ta aman jinni.
Na garzaya can da safe, amma na samu da na ba ya ma iya magana. Daga nan sai
suka amince su bayar da belin sa. Na garzaya da shi asibiti, inda a can ya
rasu.” Inji Abdullahi.
“Daga
nan sai na kai kara a Babbar Kotun Kano. Kotu ta yanke hukuncin cewa su biya ni
diyyar naira milyan 10, amma har yau ba su biya ba. Kuma tun cikin 2015 aka
yanke hukuncin.”
“Yan
sanda sun daukaka kara, aka kira ni sau daya kawai, daga nan shari’ar ta mutu.”
Abdullahi
ya bayyana wa BBC cewa a lokacin Hassan ya samu karo karatu a Jami’ar Eagypt kafin
mutuwar ta sa.
“Yanzu
haka ma ina nan tare da takardar daukar sa jami’ar da kuma bizar shirin tafiyar
sa Egypt din. Tun daga abin da SARS suka yi wa da na, har yau ban koma daidai
cikin hayyaci na ba.
Da
aka tambaye shi dangane da umarnin da Mukaddashin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo
ya bayar na a yi wa SARS garambawul, sai Abdullahi ya ce, duk wani canji in dai
canjin suna ne kawai, “ai zancen banza ne.”
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku