MNANGAGWA YA KARBI RANTSUWAR SHUGABANCIN ZIMBABWE
Jiya Lahadi aka rantsar da Emmerson Mnangagwa a matsayin
sabon shugaban Zimbabwe bayan lashe zaben shugabancin kasar da ya gudana a
watan Yuli, zabe na farko bayan shudewar mulkin shekaru 37 na Robert Mugabe.
Bayan karbar rantsuwar kama
aiki a filin wasanni da ke birnin Harare, Mnangagwa, ya sha alwashin kare
mutunci da hakkokin ‘yan Zimbabwe, inda ya ce gwamnatin za ta mayar da hankali
sosai wajen dai-daita tattalin arzikin kasar da ya dade da durkushewa.
Mnangagwa ya kuma yi alkwarin kadamar da bincike kan rikicin
siyasar kasar da ya biyo bayan zanga-zangar 'yan adawa da suka ki amincewa da
sakamakon zaben shugabancin kasar, bayan kammala shi.
A jiya Asabar ne dai, yayin mayar da martani kan hukuncin kotun
kolin Zimbabwe da ta tabbatar da nasarar Mnangagwa, Jargoran ‘yan adawa Nelson
Chamisa ya sha alwashin cigaba da kalubalantar sakamakon zaben, tare da kuma
jagorantar jerin zanga-zangar lumana a kasar.
Tsohon shugaban Zimbabwe Robert Mugabe bai samu halartar bikin
rantsar da Mnangagwa ba, sai dai 'yarsa Bonu ta wakilci tsohon shugaban,
wadda a baya ta bayyana Mnangagwa a matsayin maci amana, bayan kawar da mulkin
mahaifinta.
Idan za'a iya tunawa dai Shugaba Mnangagwa wanda ya tsayawa
jam'iyyar ZANU-PF mai mullki takara, ya lashe kashi 50.8 na kuri'un da aka kada
a zaben da ya gudana a ranar 30 ga watan Yuli, yayinda jagoran 'yan adawa
Nelson Chamisa ya samu kashi 44.3 na kuri'un.
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku