MATAIMAKIN SHUGABAN APC NA OSUN YA JAGORANCI MUTANE 6,208 ZUWA ADP


















Mataimakin shugaban jam’iyyar All Progressives Congress a jihar Osun, Azeez Adesiji, ya jagoranci mambobin kwamitin jam’iyyar na jihar su takwas da mambobin jam’iyyar 6,200 na kananan hukumomi da mazabu zuwa jam’iyyar Action Democratic Party.



Shugabannin APC da mabiyansu sun samu tarba daga shugaban jam’iyyar APD, Toye Akinola a sakatariya jam’iyyar dake Osogbo cikin farin ciki. Adesiji yayi zargin cewa dalilin su na sauya sheka ya kasace saboda son kai da halin rashi kula na masu yanke hukunci a APC da kuma yadda gwamnatin jhar ke yi da jama’a ajihar. Shugaban jam’iyyar ADP a jihar, Toye Akinola yace ya ji dadin sauya shekar yan siyasa daga jam’iya mai mulki zuwa jam’iyyar adawar.
Yace wasu yan jam’iyyar APC sun sanar da shi cewa suna nan dawowa jam’iyyar kwanan nan. Ya bukaci mutanen jihar da su marawa dan takarar gwamna a jam’iyyar Moshood Adeoti vaya domin cewa shine zai ceto su daga wahalhalun da suke ciki.



DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/

ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html

Comments