KWASTAM TA KAMA WANI BABBAN SUNDUKI DA YA SHIGO NAJERIYA MAKARE DA KAKIN SOJOJI
Hukumar yaki da fasa kauri, wanda aka fi sani da
suna Kwastam ta cafke wani babban sunduki da aka shigo dashi Najeriya makare da
kayan sawan Sojoji da dama, inji rahoton jaridar Punch.
mataimakin shugaban kwastam na yankin Fatakwal,
Sanusi Umar ne ya sanar da haka a ranar Alhamis, 16 ga watan Agusta, inda yace
kayan sun hada da wando da rigan Kaki guda 620, kanaan riguna yan ciki na Soja
guda 10,100 sai kuma takalman Sojoji kafa 512.
Kwantrola Sanusi yace: “A yau mun kama wani sunduki mai lamba MRKU 4909151 dake cike makil da
kayan sawan Sojoji, mallakin kamfani Ehiogocho Nigeria Limited, kamfanin da
muka kama ta da shigo da sunduki cike da kayan Sojoji mako biyu da suka gabata,
mai kamfanin shine Ongwatabo Jerry.
“Bincikenmu ya nuna akwai kayan Sojoji a cikin sundukin da suka hada da
wando da rigan Kaki guda 620, kanaan riguna yan ciki na Soja guda 10,100 sai
kuma takalman Sojoji kafa 512, wanda hakan haramun ne a Najeriya bisa dokokin
hukumar Kwastam.” Inji shi.
Daga karshe anyi canjin shugabanci, inda
kwantrola Abubakar Bashir ya mika ragamar mulki ga sabon kwantrola Saidu
Galadima, inda Galadima ya ja hankalin jami’an kwastam dake yankin dasu guji
cin hanci da rashawa, kuma su yi aiki da kishin kasa.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku