HUKUMAR ZABEN CONGO TA SOMA TATTANCE 'YAN TAKARA
A Jamhuriyar Dimokkuradiyar Congo yan takara a
zaben Shugabancin kasar 26 ne suka samu yi rijista tareda gabatar da takardun
su zuwa hukumar zaben kasar. A daya geffen Shugaban kasar Joseph Kabila ya
bayanna cewa ba zai tsaya takara ba, matakin da kasashen Duniya suka yaba da shi.
Bayan da kasashen Duniya
suka soma nuna farin cikin su bayan janyewar Shugaban kasar Joseph Kabila da
sake neman takarar shugabancin Congo,
tun ranar 2 ga watan Agusta ne kotuna na musaman suka mayar da
hankali domin fayyace daya bayan daya takardun yan takara 59.139 a zaben
wakilan majalisa da zai gudana ranar 23 ga watan disemba, bayan haka dai ne
hukumar zaben kasar za ta mayar da hankali ranar 11 ga wannan watan domin fitar
da sunayen yan takara da suka dace su tsaya neman kujerar majalisa.
Bangaren takara na Shugabancin kasar yan takara 26 ne suka samu
yin rijista , yan takara da suka hada da Antoine Gizenga, Adolphe Muzito, Amy
Badibanga, Emmanuel Ramazani na kusa da Shugaban kasar kuma ministan tsaro,
Felix Tshisekedi, Vital Kamere, Michel Okongo, Jean Pierre Bemba.
Daya daga cikin masu adawa da Shugaban kasar tsohon gwamnan
Katanga Moise Katumbi da hukumomin suka haramtawa shiga kasar bai samu damar
gabatar da takardun sa zuwa hukumar zabe ba, wanda magoya bayan sa ke ci gaba
da yi tir da Allah wadai gani matakan tsaro da hukumomin suka dauka a kan
iyakar kasar da Zambia don hana shi shiga kasar.
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku