BUHARI BA ZAI HUTA BA HAR SAI AN DAWO DA LEAH SHARIBU DA SAURANSU GIDA - INJI FADAR GWAMNATI

 MURYAR LEAH SHARIBU GA GWAMNATI DA AL'UMMAN NAJERIYA

- Fadar shugaban kasa tayi martani akan maganar da Yar makaratan Dapchi tayi
- Ta bukaci gwamnati ta ceci rayuwarta
- Fadar shugaban kasar tace Buhari ba zai huta ba har sai ya ceto Leah da sauran mutane

Fadar shugaban kasa tayi martani akan wani faifan Magana dake yawo na muryar aka ce mallakar Leah Sharibu ne inda ta bukaci gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kawo mata tallafi. A wata sanarwa daga Garba Shehu wanda ya kasance babban mai ba shugaban kasa shawara na musamman a kafofin watsa labarai da shafukan zumunta a ranar Litinin, 27 ga watan Agusta, yace shugaban kasar na sane da faifan muryan sannan kuma cewa jami’an sirri na aiki akai.


Shehu yace gwamnatin ta mayar da hankali waje dawo da Leah da sauran mutan da yan Boko Haram suka sace gida.

eah Sharibu ce kadai ba’a saki ba lokacin da aka saki sauran yan matan saboda ta ki sauya addininta zuwa Musulunci. A wani hoto da odiyo na nuna cewa tana da rai. Jaridar The Cable ta samu rahoto na musamman da ya kunshi hotonta da gajeren jawabi. 


 DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA  

Comments