HRW TA CE ANA MUZGUNAWA 'YAN JARIDA A NAJERIYA
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta zargin hukumomin tsaron Najeriya da tursasawa ‘yan jarida a kasar, inda kungiyar ke cewa matakan da hukumomin tsaron ke dauka sun haddasa tsoro ga ma’aikatan yada labarai.
Misis Anietie Ewang daya daga
cikin manyan jami’ai a Kungiyar, ta ce kama dan jarida tare da jefa shi a gidan
yari, ba abin da zai haifar face komabaya ta fannin bai wa jama’a damar sanin
abin da ke faruwa.
Human Rights Watch ta ce yanzu
haka akwai wani dan jarida mai suna Jones Abiri da ke aiki da Jaridar Weekly
Source Newspaper, wanda hukumar DSS ta cafke shekaru biyu ba tare da an yi masa
shari’a bisa zargin cewa yana da alaka da ‘yan bindiga na yankin Niger Delta.
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku