GWAMNATIN LEGAS TA BUDE GADAR THIRD MAINLAND BRIDGE
Gwamnatin Legas a Najeriya,
ta bude babbar gadar da ta sada yankin tsibiri da kan tudun jihar ta kan ruwa,
wato Third Mainland, wadda aka rufe ta a daren ranar Alhamis da ta gabata.
A ranar Lahadi, 26 ga Agusta gwamnatin ta Legas ta sanar da cewa da misalin karfe 5 na yammaci za ta bude gadar.
An dai rufe katafariyar gadar ce, domin gudanar da bincike kan ayyukan sake karfafata da yakamata ayi, gwaje-gwajen da zuwa yanzu, injiniyoyi suka kammala, a cewar babban sakataren ma’aikatar Sufurin jihar ta Legas, Dakta Taiwo Salaam.Rufe gadar na gajeren lokaci dai ya haddasa samun cinkoson ababen hawa, a hanyoyin da suka koma bi domin zirga-zirga tsakanin manyan yankunan kan tudu da kuma tsibirin da ke jihar ta Legas.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html

Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku