DAKARUN SOJI SUN YI NASARAR KWATO KANANAN YARA 23 DAGA HANNUN KUNGIYAR BOKO HARAM
Hukumar
Sojin Najeriya ta mika kananan yara 23 data ceto daga hannun Boko Haram da
jami'an Asusun yara ta majalisar dinkin duniya (UNICEF) domin a basu kullawa na
musamman kafin a mayar dasu hannun iyayensu su cigaba da rayuwa cikin jama'a.
Kwamandan Operation Lafiya dake aikin samar da
tsaro a Arewa maso gabas, Manjo Janar Abbah Dikko ne ya bayar da wannan
sanarwan a hedkwatan hukumar dake Maiduguri inda yace sunyi hakan ne domin haka
ka'idar take a dukkan kasashen duniya. Dikko ya ce, "Kamar yadda dokar
aikin soji na duniya ta tanada, mun mika wadannan yaran da suka dade hannun
mayakan kungiyar ta'addan Boko Haram ga kungiyar UNICEF.
A jawabinsa, Mr Geoffrey Ijumba na ofishin
UNICEF da ke jihar Borno ya yi maraba da yaran wanda shekarunsu ke tsakanin 12
zuwa 17.
Ya ce UNICEF na aiki tare da Hukumar Sojin
Najeriya da Ma'aikatan Harkokin Mata na jihar Borno domin samar da bayar da
magani ga mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa da basu kulawa ta musamman. Ya
ce, "Daga yau zamu fara bawa yaran nan kulawa ta musamman domin ganin cewa
nan da wani lokaci zasu iya komawa wajen iyalensu domin cigaba da rayuwa cikin
jama'a. Pernille Ironside, wakilin UNICEF na wucin gadi, ta jadada cewa UNICEF
zata cigaba da aiki tare da Hukumar Sojin Najeriya da sauran hukumomi domin
taimakawa dukkan yaran da aka ceto daga hannun Boko Haram. Ironside ta kara
bayyana muhimmancin bawa yaran gudunmawa domin su cimma burin da suka sanya
gaba a rayuwa inda tace hukumar ba zata yi kasa a gwiwa ba har sai taga dukkan
yaran sun koma gida wajen iyalensu kamar yadda NAN ta wallafa.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku