BUHARI YA YI GANAWA TA MUSAMMAN DA SHUGABANNIN RUNDUNONIN TSARON KASAR NAN
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya
gana da shugabannin rundunonin tsaron kasar nan a fadar sa ranar Litini.
Makasudin wannan ganawa kuwa shine
domin a tattauna halin da ake ciki musamman abin da ya shafi tsaro a kasar nan
da kuma yaki da Boko Haram da ake yi a yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya.
Shugaba Buhari ya hore su da su maida hankali matuka a aikin su
sannan su tabbatar ana samun nasara a ayyukan tsaro da aka sa a gaba.
A Lahadin da ta gabata Boko Haram sun kai hari kauyen Mailari dake
yankin Guzamala a jihar Barno inda akalla mutane 19 suka rasu a sanadiyyar
wannan hari.
Sai dai wani ma’aikacin sansanin ‘yan gudun hijira da ke yanki da
ba ya so a fadi sunan sa ya bayyana cewa a dalilin wannan hari mutane 63 ne
suka rasa rayukan su.
Da ya ke tofa albarkacin bakin bayan ganawar, ministan tsaro
Mansur Dan-Ali rundunonin tsaro na kasa za su ci gaba da yin aiki tukuru domin
ganin an sami wanzuwar zaman lafiya a kasa Najeriya.
” Dakarun Najeriya suna kokarin gaske a musamman jihohin Zamfara,
Benuwai, Kaduna da sauran sassan kasar nan, za a ci gaba maida hankali wajen
ganin an kau da ayyukan masu tada zaune tsaye a fadin kasar nan.” Inji Dan-Ali.
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku