BUHARI YA YI FATAN ALKHAIRI GA MASU SAUYA SHEKAR SIYASA A NAJERIYA
Shugaban Najeriya Muhammadu
Buhari ya aike da sakon fatan alkhairi ga Ilahirin ‘yan siyasar da suka sauya
sheka daga wata jam’iyyar zuwa wata a dai dai lokacin da babban zaben kasar ke
karatowa.
Muhammadu Buhari yayin wani
taron cin abinci rana da ya gudana tsakaninsa da gwamnonin Jam’iyyar ta APC ya
ce kowanne dan siyasa na da dalilin sauya sheka zuwa wata Jam’iyya.
A cewar shugaban na
Najeriya, sauya shekar ta wasu jiga-jigan siyasa a kasar ba zai kawo tsaiko ga
ayyukan da gwamnatinsa ke yi don gina kasar ba.
A baya-bayan nan ne dai
wasu tarin jiga-jigan Jam’iyyar ta APC suka sauya sheka zuwa babbar Jam’iyyar
adawa ta PDP ciki kuwa har da shugaban Majalisar Dattijan kasar Bukola Saraki.
Sauran wadanda suka sauya
shekar sun hada da Samuel Ortom Gwamnan Benue da Abdulfatah Ahmed Gwamnan Kwara
da Godswill Akpabio tsohon Gwamnan Akwa Ibom.
Galibin dai masu sauya
shekar sun nuna rashin amincewa da salon mulkin Muhammadu Buhari wanda ya karbi
shugabancin a shekarar 2015.
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku