ANA GUDANAR DA BUKUKUWAN SALLAR LAYYA A SASSAN DUNIYA
Musulmi a sassa daban daban na
duniya na gudanar da bukukuwan babbar sallah ko kuma sallar layya, bayan da
mahajjata suka sauka daga hawan Arafat.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
na gudanar da bukukuwan sallar ne a garinsu na Daura da ke arewacin kasar, inda
rahotanni ke cewa shugaban ya taka da kafa har tsawon mitoci 800 domin dawowa
gida bayan kammala sallar ta idi.
A jihar Kano kuwa, rahotonni sun
ce gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje, ya yi amfani da wannan rana domin
‘yantar da wasu fursunoni da yawansu ya kai 170 daga gidan yarin Goron Dutse,
tare da bai wa kowanne daga cikinsu Naira dubu biyar a matsayin kudin mota
domin komawa garuruwansu.
To sai dai a makociyar Najeriya
wato Jamhuriyar Nijar, sai a gobe laraba ne za a gudanar da bukukuwan babbar
sallar ta bana.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku