AN SAKI LAWAL DAURA, AMMA AN KWACE MASA FASFO
Jami’an leken asiri sun saki korarren Babban Daraktan DSS, Lawal
Daura, bayan an kwace masa fasfo. Haka wata majiya ta shaida wa jaridar PREMIUM
TIMES.
An sako shi ran Laraba da yamma, daga gidan da ya ke a tsare,
wanda jami’an SSS ne ke kula da shi, a Gwarimpa. A can ya ke tsare tun lokacin
da Mukaddashin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya bada umarnin a sallame shi daga
aiki.
An bada umarnin a tsare shi bayan wasu zarge-zargen da aka ce ya
aikata wasu laifuka da suka shafi cin amanar kasa da kuma kawo barazana ga
tsaron kasa.
Da farko an bayar da rahoton cewa ya na tsare ne a
Guzape, can a ofishin SARS a Abuja, inda ya dade ya na amsa wasu muhimman
tambayoyi a hannun ‘yan sanda.
Daga nan kuma an rika yawo da shi, daga wannan gida
zuwa wancan a cikin Abuja. Daga nan an adana shi a wani gida da ke Gwarimpa,
haka wata majiyar jami’an tsaro ta shaida wa jaridar PREMIUM TIMES.
“An damka masa wayar tarho din sa, kuma aka ce ya
tafi abin sa. Amma an kwace masa fasfo, yadda ba zai iya fita kasashen waje
ba.”
“Ba a san takamaimen inda ya ke ba, amma dai babu
yadda za a yi ya iya sulalewa ya gudu, tunda akwai sa-ido sosai a kan sa.”
Ana kuma sa ran zai fuskanci caji daga tuhumar da
ake yi masa.
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku