AN KASHE SHUGABAN KUNGIYAR 'YAN TA'ADDAN ISIS A AFGHANISTAN
- Kasar Amruka ta kashe shugaban kungiyar ISIS
na Afghanistan ta hanyar kai hari maboyarsa
- Shi ne shugaban kungiyar ISIS na uku da aka
kasha a Afganistan cikin shekaru biyu
- Kasar Amruka ta sha alwashin ci gaba da yaki
da kungiyoyin ta’ddanci dake a waje da cikin kasar ta.
Jami’in kasar Amruka ya sanar da cewa, an kashe
shugaban kungiyar ‘yan ta’addatan ISIS, wanda yayi shirya tashin wasu bama
bamai da suka yi sanadin mutuwar daruruwan mutane a Afghanistan, bayan da
Amruka ta kai hari a mabuyarsa.
“Mataimakin
mai Magana da yawun shugaban kasar Afghanistan, Ashraf Ghani ne ya sanar da mu
mutuwar shugaban kungiyar ta ISIS-K, Abu Sayeed Orakzai”, a
cewar jami’in Amrukan, Col. Martin O’Donnell. Cikin wata sanarwa, O’Donnell ya
ce: “Haka zalika nima zan kara da cewa,
Amruka na ci gaba da yaki da kungiyoyin ‘yan ta’adda kamar su ISIS-K, Al-Qaeda,
da dai sauran kungiyoyin ciki da wajen,”
Rahotanni sun bayyana cewa An kai harin ne a
yankin Nangarhar, kusa da iyakar kasar Pakistan, inda yai sanadin mutuwar wasu
dakarun rundunar ISIS guda 10. Shi dai Orakzai, shi ne kusan shugaban kungiyar
ISIS-K na uku da aka kashe a Afghanistan a cikin shekaru biyu. Kungiyar ta ISIS
ta rasa iko akan wasu garuruwa da ke da iyaka da kasashen Iraq da Syria tun
fara rikicinsu a watan Yulin 2014.
Kisan Orakzai ya biyo bayan wani sakon sautin
murya da babban shugaban kungiyar ta IS, Abu Bakr al-Baghdadi ya fitar, inda
yake sam barka ga mabiyansa da taya su murnar bukin babbar Sallah Har yanzu
ba’a san mabuyar Al-Baghdadi ba tun bayan shaharar kungiyar ta IS. Ya dai taba
fitowa fili a shekara ta 2014 a wani gari dake arewacin Iraqi, inda daga bisani
akai ta yayata jita jitar mutuwarsa.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/ TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku