AN KAMA MASU GADIN DA SUKA SACE NAIRA MILIYAN N5M A WANI ASIBITIN JIHAR BORNO
- Son abin Duniya ya kai wasu masu aikin gadi
ya baro
- Zuciyarsu ta yaudare su sun saci makudan
kudade a wurin aikinsu
- Sai dai tuni 'yan sanda suka zabaro su bayan
sun kashe kudaden
Jami'an rundunar ‘yan sanda ta SARS sun kame
wasu masu aikin gadi bisa zarginsu da sace kudi kimanin Naira miliyan biyar a
asibitin kwararru dake Maiduguri.
Wata majiya mai karfi ta bayyanawa kamfanin
dillanci labarai na kasa (NAN) cewa an kame wadanda ake zargin ne ranar Asabar,
sakamakon binciken da jami'an tsaro suka gudanar.
Kamfanin dillancin labaran ya
rawaito cewa barayin sun samu nasarar sace kudin ne ta hanyar shiga ofishin
ma’ajin kudi ta saman rufin kwanon, inda ta nan suka sace makudan kudin. “Bayan
sun sace kudin sun sayo Mota ta sama da Naira miliyan biyu, tare kuma da
garzayawa jihar Kano inda suka kashe kudin. Bayan da su ka batar da kudin ne,
sai suka sayar da motar". Da ya ke tofa albarkacin bakin sa akan faruwar
lamarin shugaban asibitin Dakta Laraba Bello, ya ce barayin da suka yi wannan
satar masu Gadin su ne.
“Ranar daya ga watan Mayu, ma’ajin kudin
asibitin ya zo aiki, kawai sai ya tarar da ma'ajiyar kudi a karye, amma kuma
kofar a rufe take".
Ya kara da cewa wannan al'amarin ya jefa
ma'aikatan asibitin cikin firgici da tashin hankali A nasa bangaren shugaban
kamfanin samar da masu gadi na HIM Global Nigerian Security Mista Babatunde
Satomey, ya bayyana cewa tuni kamfanin ya dauki matakin korar wadanda suka
aikata laifin. “Gaba dayansu mun sallamesu daga bakin aiki, domin sabawa dokar
aiki da suka yi" A karshe ya tabbatar da cewa sun hada kai da rundunar
tsaron ta farin kaya , DSS da Sojoji domin aiki tare da cigaba da samar da
amintattun gadi, tare da bankado baragurbin.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku