AN HANA MAGATAKARDAN MAJALISAR DOKOKIN KASAR SHIGA MAJALISA



Yayinda ake ci gaba da yiwa majalisar dokokin kasar kawanya, an hana magatakardan majalisar dokokin kasar, Alhaji Mohammed Sani Omolori, shiga majalisar.

Oolori ya isa zangon majalisar dokokin da misalin karfe 10:02 na safe, amma jami’an DSS da suka yiwa waje kawanya sun hana shi shiga majalisar. 


A yayinda magatakardan ya isa majalisar dokokin, ya tunkari jami’an DSS din kan dalilin da yasa aka haa ma’aikatansa da sauran mutane shiga harabar.


Sai suka maida masa da martanin cewa suna yin yadda aka umurce su ne daga sama. Sai ya juya cikin fushi ya bar wajen amma yayi jawabi ga ma’aikatan majalisar dokokin inda ya bukaci su kwantar da hankalinsu kamar yadda bai san mai ke faruwa ba.



Ya kuma gargade su da kada su dauki doka a hannunsu, inda ya tabbatar masu da cewa baya da hannu cikin abunda ke faruwa.




DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/

ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html

Comments