AMBALIYAR RUWA TA LALATA GONAKIN SHINKAFA A SOKOTO


Ambaliyar ruwa ta lalata gonakin shinkafa a kauyuka 10 dake jihar Sokoto, abinda ya tilastawa manoman kwashe amfaninsu ba tare da lokacin hakan ya yi ba.



Lamarin ya samo asali ne sanadiyar bude madatsar ruwan Bakalori ba tare da sanar da manoman Jihar ta Sokoto ba.
Wakilinmu a Sokoto Faruk Muhammad Yabo ya ziyarci wasu manoma da ambaliyar ta shafa, kamar yadda za’a saurara a rahoton da ya aiko mana.

DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 



Comments