ALHAZAN NAJERIYA UKU SUN RASU A HADARIN MOTA A KUSA DA MADINA
Shugaban kula da lafiyar Alhazai
na hukumar NAHCON Ibrahim Kana ya tabbatar wa manema labarai cewa wasu alhazai
daga jihar Zamfara sun rasu a hadarin mota daga Madina zuwa Makka a safiyar
Juma’a.
Alhazan
da suka rasu sun hada da Shinkafi Mudi Mallamawa, Abdullahi Jafaru Gidan
Sambo,da Abdullahi Shugaba.
An
aika da gawarwakin wadannan Alhazai da suka rasu asibitin Sarki Fahad dake
Madina, inda sauran wadanda suka ji ciwo aka kwantar dasu a wani asibiti dake
kusa da Madinna.
Shugaban
kungiyar ‘yan jarida na jihar Zamfara Abdulrazak Kaura da shi ma yanzu haka
yana kasar Saudi ya ce dukkan wadanda suka rasu shugabannin jam’iyyar APC ne a
kananan hukumomin Zamfara.
”
Jafarau Gidan Sambo shine shugaban APC na karamar hukumar Kaura Namoda, Mudi
Mallamawa na Shinkafi sannan Abdullahi Shugaba na Karamar hukumar Maru.”
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku