ZA A HUKUNTA MA’AIKACIN DAKE YIN WURU-WURU A ASIBITOCIN JIHAR KUROSS-RIBAS
Gwamnatin jihar Cross River ta gargadi ma’aikatan asibitocin
jihar cewa kowa ya shiga taitayin sa domin kuwa za ta hukunta duk ma’aikacin
asibiti da aka kama yana karban kudi fiye da maralafiya ya kamata ya biya da
gwamnati ta riga ta kiyasta.
Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na jihar Betta
Edu ya bayyana haka inda ya kara da cewa gwamnati ta kuma kafa kwamiti domin
ganin an bi wannan doka sau da kafa.
Ya kuma kara da cewa gwamnati za ta hukunta duk wani ma’aikaci
da baya zuwa aiki akan lokaci ko kuma ya ke kin zuwa.
Ya ce dole ma’aikata asibitocin jihar lallai su maida hankali
wajen ganin aikin su ne kawai a gaban su ba yi wa gwamnati zagon kasa ba da
jikkata marasa lafiya.
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku