'YAN BINDIGA SUN HARBE BABBAN LIMAMI A JIHAR FILATO
A daren ranar Laraba ne wasu 'yan bindiga da
ba'a san ko su wanene ba suka harbe babban limamin garin Bachi dake karamar
hukumar Riyom na jihar Filato. Marigayi Alhaji Abdullahi
Abubakar ba boyeye bane a jihar musamman yadda
ya yi suna wajen kira a zauna lafiya da kuma hallartan taron sulhu tsakanin
Fulani da 'yan kabilar Birom da masu sassan jihar. Shugaban kungiyar Miyetti
Allah na jihar, Alhaji Ibrahim Mato, ya shaidawa Daily Trust cewa marigayi
Abubakar mutum ne mai son zaman lafiya da hadin kan al'umma hakan yasa kowa ke
mutunta shi.
Ya ce 'yan bindigan sun kutsa kai ne cikin
gidan babban malamin misalin karfe 10 na dare kuma suka harbe shi har lahira.
Jami'an yadda labarai na Operation Safe Haven, Manjo Adam Umar, yace shugaban
kungiyar Miyetti Allah na Riyom na kawo masa rahoton rasuwar. Ya kara da cewa
jami'an hukumar sojin sun fara gudanar da bincike tare da 'yan sanda don ganin
an gano wadanda suka aikata wannan mummunan aikin.
A wani rahoton, NAIJ.com ta
kawo muku rasuwar tsohon Sufeta Janar na Yan sandan Najeriya, Alhaji Ibrahim Coomassie,
marigayin ya rasu ne a jihar sa ta Katsina bayan ya yi fama da gajeruwar rashin
lafiya. Anyi jana'izar Coomassie a ranar Juma'a 20 ga watan Yulin shekarar 2018
a jihar Katsina.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku