YADDA DINO MELAYE YA TSERE BAYAN AN SACE SHI
Sanata da ke
wakiltar Kogi ta Yamma Dino Melaye ya bayyana yadda ya tsira daga fafurar da
wasu ‘yan taratsi suka kai masa a hanyar Abuja zuwa Lokoja a makon da ya
gabata.
A doguwar hira da ya
yi da PREMIUM TIMES yace wasu motoci uku ne suka afka gaban sa a hanyar sa ta
zuwa Lokoja domin amsa gayyatar Kotu.
” Ina tafiya na salin-alin sai kawai wasu motoci uku
suka shigo gabana da ya sa dole na taka burki na tsaya.
” Tsaya wa na ke da wuya sai suka nemi su bude mini
wuta da bindigogi, amma kuma mota ta bindiga baya huda ta. Daga nan sai suka
fara ihu suna cewa ‘mu kona shi a cikin motar, mu kona shi a motar.’ Sai suka
tsallaka titi neman taya da itatuwa domin su babbake ni a cikin motar.
” Ana haka ne fa ni kuma na yi wuf na fito daga
cikin motar na arce cikin kungurmin daji, suka ko biyo ni da gudun tsiya, amma
kafin su tadda ni na dare wata itaciya na yi shiru abina.
” Ina saman wannan bishiya sai na hango su sun wuce
ni da gudu suna nema na. Na yi shiru tsit sai naga sun dawo sun koma da baya.
Dino ya kara da cewa a haka ne ya makale a can saman
bishiyar har tsawon awa 11. Sai da ya tabbatar sun tafi sannan ya sakko ya kama
gaban sa.
Ya ce zai iya gane motocin da suka bishi, domin ya
ga wadannan motoci a kotu a Abuja ranar Laraban makon da ta gabata.
” Ina tabbatar muku da cewa wannan shiri ne da hadin
bakin ‘yan sanda. Kuma idan ma an kashe ni, gobe irina 100 za su bayyana don ci
gaba da gwagwarmaya.
“Ba zan gaji da fadin aibin mulkin Buhari ba”
Dino yace ya nemi a samar masa da jami’an tsaro na
‘Civil Defence’ amma an ki ba shi sabo da fin karfi.
” Kiri-kiri a matsayina na sanata a Najeriya amma an
hanani jami’an tsaron da za su rika kula da ni, balle kuma sauran ‘yan
Najeriya.”
Dino dai ya fadi cewa wannan abu ya faru ne a gaba
kadan da garin Gwagwalada a hanyar sa ta zuwa Lokoja daga Abuja.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku