WANI DAN TSIBU MAI SHEKARU 23 YA YIWA WATA YAR SHEKARU 29 FYADE


- Hukumar Yan sanda ta kama wani dan tsibu mai shekaru 23 bisa zarginsa da yiwa wata yar shekaru 29 fyade.



- Dan tsibun mai suna Mustapha Hammed, ya yiwa matar karyar cewa anyi masa wahayin cewa zata mutu



- Ya kuma shaidawa matar cewa za'a iya kawar ta mutuwar nata idan a kayi mata wankan tsarki kuma ta amince da hakan Hukumar Yan sandan Najeriya reshen jihar Legas ta kama wani dan tsibu mai shekaru 23 mai suna Mustapha Hammed saboda zarginsa da yiwa wata dalibar Kwallejin Ilimin Fasaha dake Akoka Legas fyade.
Punch ta ruwaito cewa Hammed ya fadawa dalibar cewa ya gano cewa zata mutu cikin sa'o'i 24 muddin ba ta amince anyi mata wankan tsarki ba.
NAIJ.com ta tattaro cewa an tafi da dalibar unguwar Itowolo dake yankin Ikorodu dake Legas inda za'ayi mata wankan tsarkin. A yayin da yake yiwa manema labarai jawabi a ranar Litinin 16 ga watan Yuli, kwamishinan Yan sandan Legas, Edgal Imohimi yace: "Dan tsibun ya yaudari dalibar cewa ya gano zata mutu cikin sa'o'i 24. Ya kaita Ikorodu dake Legas don yi mata wankan tsarki amma yayi mata fyade duk da cewa yarinyar bata taba saduwa da na miji ba. "Mahaifin yarinyar yace tun bayan afkuwalar lamarin, yarinyar ta fita hayyacin ta kuma tana cikin damuwa game da abinda dan tsibun ya aikata gareta." Wanda ake tuhumar, dan asalin jihar Oyo, ya amsa cewa shi ne ya kawar wa yarinyar da budurcinta bayan ya sadu da ita a gidansa dake Ikorodu don yi mata wankan tsarki. Kamar yadda kwamishina Yan sandan ya bayyana, a halin yanzu an tura binciken lamarin zuwa sashin kula da jinsi na hukumar don cigaba da bincike. Ya kuma ce za'a gurfanar da wanda ake tuhuma gaban kotu bayan an kammala binciken.


DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com 

Comments