TARON GANGAMIN GOYON BAYAN BUHARI A JIHAR AKWA IBOM - HOTUNA


A ran Asabar, ne dubun dubatan mutane a jihar Akwa Ibom suka gudanar da wani taron gangamin nuna goyon bayansu ga takarar shugaba Buhari a zaben 2019.



A dai jihar ta Akwa Ibom dake kudu maso kudancin Najeriya, sabon shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole, ya karbi wasu tsofin 'yan majalisar wakilai 2 da magoya bayansu fiye da 20,000 da suka fice daga jam'iyyar PDP. Tsofin 'yan majalisar su ne; Bassey Etim da Esio Okwong. Sun kasance a majalisar ta wakilai ne daga shekarar 2003 zuwa 2007.


Oshiomhole ya karbi tsofin 'yan majalisar ne a sakatariyar jam'iyyar APC dake Uyo, babban birnin jihar ta Akwa Ibom. A jawabinsa ga sabbin 'yan APC din, Oshiomhole ya bukaci hada kai da tsofin 'yan jam'iyyar domin samun nasara a zabukan shekarar 2019.



DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com

Comments