SHUGABA BUHARI A TARON GANGAMIN AU A MAURITANIA
Shugaban kasan Najeriya, Muhammadu Buhari, na halartan taron
gangamin gamayyar shugabannin kasashen Afrika karo na 31 da ake yi yau Lahadi,
1 ga watan Yuli a Nouakchott, babban birnin kasar Mauritania.
Daga cikin jami'an gwamnatin Najeriyan da ke tare da shi a
taron sune babban lauyan tarayya kuma ministan shari'a, Abubakar Malami da
ministan harkokin wajen Najeriya, Gepffrey Onyeama.
Daga cikin wadanda suka jira saukarshi a babban filin jirgin
saman Nouakchott sune shugaban kasar Mauritania, Mohammed Ould Abdel Aziz, da
wasu manyan jami'an gwamnatin kasar.
Taron na wannan shekaran dai na ke take : “Samun nasara kan
yaki da rashawa: Yadda za’a kawo sauyi nahiyar Afrika”. Shugaba Muhammadu
Buhari ne zai gabatar da jawabi na musamman akan wannan take. Sannan shugaban
gamayyar kasashen Afrikan kuma shugaban kasan Ruwanda, Paul Kagama, zai gabatar
da jawabi kan sauye-sauyen gamayyar, shi kuma shugaban kasan Nijar, Mahamadou
Issoufou, zai gabatar da nasa kan kasuwanci a Afirka.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta
Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku