SARAKI, DOGARA, KWANKWASO ZA SU KAFA SABUWAR APC ‘NAPC.
Idan dai ba wani canjin shawara aka samu ba, a yau dinnan ne
wasu jiga-jigan jam’iyyar APC da ya hada da shugaban majalisar dattawa Bukola
Saraki, shugaban Majalisar Wakilai da tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa
Kwankwaso za su kafa sabuwar kungiya mai suna sabuwar APC, nAPC.
Sakataren kungiyar kuma tsohon jigo a jam’iyyar Muhammadu Buhari
na CPC a wancan lokaci, Buba Galadima ya sanar mana cewa lallai akwai abu mai
kamar haka da zai faru amma dai baya so ya fadi abin kafin a bayyana shi.
Bayanai sun nuna cewa hakan na da nasaba da shirin da wadannan
gungun jigajigan ‘yan siyasa komawa jam’iyyar PDP domin tunkarar Buhari da
makarraban sa a 2019.
Idan ba a manta ba tun bayan rantsar da wannan gwamnati ne ake
ta takun saka tsakanin shugaban kasa da wadannan jiga-jigan yan jam’iyyar wanda
da yawa daga cikin su sun koka ne kan watsi da su da aka yi da kuma nuna halin
ko in kula da jam’iyyar tayi musamman shugaban kasa.
A makon da ya gabata tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Kwankwaso
ya bayyana cewa shi kadai tal, da jam’iyyar PDP za su iya kada Buhari, wanda a
martanin da gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya fitar daga baya kuwa ya bayyana
cewa ko karamar hukumar sa ma ba zai iya kawo ba a 2019.
Yanzu dai kungiyar da nan tana ganawa a tsakanin mambobin ta da
sauran ‘yan jam’iyyar APC da ke cike fam da fushi kan yadda aka mai dasu
saniyar ware.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta
Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku