ME GWAMNATI TAKE YI GAME DA HARE - HAREN BOKO HARAM ?
- A makon jiya ma sun kashe soji yayin da suke tsakar daji
kai hari a sansanin mayakan
- Musulmai sun ki bin wannan akida sun zabi dimokuradiyya duk
da ba ita sahabbai suka yi ba
A makon jiya ne, Boko Haram ta karkashe sojin
Najeriya ta sace makamai, shekaru uku bayan hawan gwamnatin APC, ko ya hakan ke
kara faruwa? An dai zabo gwamnatin APC ne musamman saboda yakar Boko Haram,
kuma sunyi rawar gani, sai dai hakan bai isa ba, domin korar Boko Haram daji da
fatattakarsu ba cin yaki bane, zasu je zasu dawo. Shugaba Muhammadu Buhari na
iya gama shekaru hudu ya fadi zabe, kuma kamar fa a cikin 'yan siyasar nan shi
kadai ne ya rage cikin 'yan mazan jiya da ka iya yaki ko tafiyar dashi, sauran
yara ne ajebo, masu neman kudi da neman suna.
Idan shugaban ya zarce kuwa, akwai sauran rina
a kaba, domin wannan na nufin za'a kwashe shekaru takwas ana kashe kudade domin
yakar ta'addanci, bayan kuma gashi wasu maluman na ci gaba da wa'azin mai
zafaffa ra'ayin jama'a. Bok Haram dai daga izala ta bullo, kuma ta gagari
gwamnati, ta kwashi almajirai ta koya musu ta'addanci. Mahaifiyar Shekau ma a
kwanan nan ta tabbatar cewa Shekau Almajiri ne da babansa limamin kauye ya kai
gabas karatu.
Tun zamanin Usmanu Danfodio ake wannan jihadi,
ake kuma samar da mayaka daga cikin Almajiirai, ko yaushe hakan zai tsaya? Ya
zuwa yanzu dai, a iya cewa shekaru uku sun isa ace an gama da Boko Haram, kamar
yadda aka sa rai a 2015. Duk da cewa an yi namijin kokari wajen korarsu daji,
hakan bai sa an iya binsu daji an gama dasu ba, wai sai dai a kore su.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku