KANNYWOOD: JARUMA ZAINAB INDOMIE TA FARKA DOMIN CIGABA DAGA INDA TA TSAYA
Shahararriyar jarumar Kannywood Zainab
Abdullahi wacca aka fi sani da Zainab Indomie na shirin dawo da sunanta a
masana’antar.
An daina jin duriyar Indomie a masana’antar na
tsawon wani lokaci bisa ga wasu dalilai. Ubangidanta Adam Zango ne ya sanar da
dawowar jarumar a shafinsa na Instagram. Ya wallafa hotunanta saboda nuna farin
cikin sa bisa biyayar da take nuna masa.
Jarumar tana daya daga cikin jarumai mata dake
kan gaba da farfajiyar kamfanin White house family wanda Adam Zango ke
jagoranta.
Zainab Indomie tana daya daga fitattun matan
kannywood da suka raya masana'antar gabanin fitowar sabbin fuskoki da ake
damawa dasu yanzu.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku