INEC ZA TA DAKATAR DA YIN RAJISTA A RANAR 17 GA AGUSTA
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta,
INEC, ta bayyana cewa za ta dakatar da ci gaba da aikin yin rajista a ranar 17
Ga Agusta, har sai bayan zaben 2019.
Hukumar
ce ta yi wannan sanarwar a cikin wata takardar manema labarai da Kwamishinan
Zabe Kuma Shugaban Kwamitin Yada Labarai da Wayar da Kai masu yin Rajista, a
Abuja.
Solomon
Soyebi, ya ce za a ci gaba da aikin karba da bayar da katin zabe har sai ana
saura mako daya kacal kafin zabe, ranar 12 Ga Fabrairu, 2019.
Shugaban
ya ce an dauki wannan mataki ne bayan da Hukumar ta tuntubi manyan masu ruwa da
tsaki a harkar zabe na fadin kasar nan.
A
cikin satin nan dai INEC ta yi taron ganawa da shugabannin jam’iyya, kafafen
yada labarai, kungiyoyin sa-kai da jami’an hukumomin tsaro.
Ya
ce dukkan masu ruwa da tsaki sun amince a samu wadatacciyar ratar lokaci daga
ranar da aka daina yin rajista zuwa lokacin zabe, ta yadda za a samu lokacin
daukar bayanai da, tattarawa da killace na duk wanda yayi rajista a kwamfuta
zuwa ranar da za a fitar masa da katin zabe.
Soyebi
ya karkare da cewa INEC zai zaburar da bangaren yada labaran sa ta yadda za a
tabbatar da cewa duk wani dan Najeriya da ke son yin rajista, ya samu ya karbi
katin rajistar sa kafin mako daya a fara zabe.
A
karshe kwamishinan ya roki daukacin ‘yan Najeriya su hada kai a samu sahihin
zabe kamar yadda INEC ta yi alkawari a jihar Osun da Ekiti da kuma zaben 2019
na kasa baki daya da aka maida hankali a kan sa.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta
Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku