HANYOYI BIYAR DA SUKA FI JANYO HADDURA A NAJERIYA
Hatsarin mota babban abu ne da ya dade yana
ciwa 'yan Najeriya tuwo a kwarya, kusan ko wace rana zaka rika samun labarun
hatsarin motoci dake faruwa a titunan Najeriya. Alkalumar Cibiyar kididiga ta
kasa (NBS) ya nuna cewa an samu hatsarin mota 11,363 a 2016 wanda ya yi
sanadiyar rasuwar mutane 5,053.
Kamar yadda kowa ya sani rashin kyawun hanyoyi
yana daya daga cikin abubuwan dake janyo hadurra a titunan Najeriya, hakan yasa
muka tattaro muku tittuna 7 mafi hadari a Najeriya.
1) Titin Kaduna-Abuja
Duk da cewa tittin Kaduna zuwa Abuja shine ya
sada babban birnin Tarayya Abuja da jihohin Arewa masu yawa, har yanzu akwai
daruruwan ramuka a titin. Idan ba'a manta ba a hanyar ce wata Hummer Bus dauke
da fasinjoji 18 tayi hatsari inda 14 suka kone kurmus.
2) Titin Abuja-Lokoja-Okene-Kabba
Wannan hnayar tayi kaurin suna wajen matafiya
saboda yawan hatsari da ake samu a hanyar. Idan mutum na son zuwa Abuja ko Ondo
da sauran jihohin Kudu maso yammacin Najeriya, dole sai yabi ta hanyar
Lokoja-Okene kuma hanyar ta lalace sosai ka kuma 'yan fashi da makami.
3) Titin Otukpo-Otukpa dake Makurdi
"Ga wadanda suka saba bin wannan hanyar,
duk lokacin da suka karato titin Otukpa-Otukpo suna cike da faduwar gaba saboda
rashin sanin abinda ka iya faruwa" kamar yadda wani marubuci ya wallafa.
Baya ga zaizayar kasa da ramuka a titin, hanyar tayi kaurin suna saboda fashi
da makami da ake a hanyar
4) Titin Legas-Sagamu-Ore-Benin
Wannan titin ya kasance titi guda da ya dade
yana ciwa gwamnatocin da suka shude a shekaru 20 da suka wuce tuwo a kwarya,
inji wani mai nazarin al'amurran yau da kullum. Ya fadi hakan ne saboda irin
rashin kyawun hanyar. Idan ba kwararen direba ba, bin wannan hanyar ba karamin
hadari bane duba da yadda akwai manyan ramuka da ka iya janyo hadari ko
fashewar taya, ka kuma masu fyade da yan fashi dake jira motar ka ta lalace su
far maka.
5) Titin Legas-Ibadan
An gina wannan hanyar ce tun 1974 kuma tsawon
ta ya kai kilomita 120 amma a halin yanzu hanyar da lalace sosai duk ta fashe.
Saboda haka ana yawan samun haddura a hanyar kuma galibi direbobin tankar
dankon man fetur ne suka fi janyo hatsarin saboda irin gudu da suke yi a
hanyar. A kididgar da FRSC ta fitar, an samu haddura 2,075 wanda ya yi
sanadiyar rasuwar mutane 775 a hanyar a shekarar 2012.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku