GWAMNAN JIHAR BENUWE YA KOMA JAM'IYAR PDP


Gwaman Jihar Benuwai Samuel Ortom ya canza sheka daga jam’iyyar APC zuwa Jam’iyyar PDP a ran Laraba.

Kakakin gwamna Ortom Terver Akase ya tabbatar wa jaridar PREMIUM TIMES haka ta wayar tarho.
Ba tun yanzu ba ake ta sauraren jin haka daga gwamna Ortom domin kuwa duk alamu sun bayyana cewa gwamnan yana gab da ya canza sheka daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP tun ba yanzu ba,
A makon da ya gabata ne gwamna Ortom ya bayyana wa ‘yan Najeriya cewa jam’iyyar APC ta bashi jan kati na ya fice daga jam’iyyar.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com

Comments