EKITI: PDP ZA TA YI ZANGA-ZANGAN LUMANA NA GAMA GARI



Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya umurci jami’an jam’iyyar na jihohi, shugabanni da masu ruwa da tsaki da su yi zanga-zangan lumana a hukumomin yan sanda dake dukkanin jihohin tarayya.


A wata sanarwa daga sakataren shirye-shirye na jam’iyyar, Kanal Austin Akobundu (mai ritaya) a jiya, jam’iyyar ta bukaci dukannin reshen tan a jihohi da su gabatar da wasikar zanga-zanga ga sufeto janar na yan sanda, Ibrahim Idris ta hanyar kwamishinonin yan sandansu.
A kwanakin baya wadansu kafan yada labarai sunruwaito cewa Kayode Fayemi, dan takarar gwamna karkashin jam’iyyar APC a zaben Ekiti da za’a yi a ranar, Asabar ya ce yana so ya sake mulkar jihar ne domin rage talauci a tsakanin mutane. Ya bayyana hakan ne a gangamin karshe da APC ta yi gabannin zaben a filin wasa na Oluyemi Kayode dake Ado Ekiti a ranar Talata, 10 ga watan Yuli. Mista Fayemi wadda ya yi gwamnan jihar daga 2010 zuwa 2014, ya bayyanawa taron jama’a cewa magajinsa, Gwamna Ayodele Fayose, ya muzgunawa jama’ar jihar ta hanyar kin biyan albashi da fansho



Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta


Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com 

Comments