DAN KUNAR BAKIN WAKE YA KAI MUMUNAN HARI MASALLACI DA ASUBAN NAN



Wani dan kunar bakin waken yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram ya kai mumunan harin kunar bakin wani masallaci da ke Konduga a jihar Borno lokacin Sallar Asuba misalin karfe 5:15 na safe.

Wata majiya ta bayyanawa jaridar The Cable cewa an hallaka masallata da dama kuma wasu sun jikkata. Yayinda jami’an tsaro suka hallaro wajen a yanzu, an garzaya da wadanda suka jikkata asibiti. A yanzu dai mutane takwas ne suka rasa rayukansu game da cewar wani dan CTJF a garin, Ibrahim Liman, wanda yayi bayani ga manema labarai. Ya bayyana cewa dan kunar bakin wake ne ya shigo masallacin misalin karfe 5:15 yayinda mutane ke Sallah ya tayar da Bam.

Yace: “Wani dan kunar bakin wake ne ya shiga masallacin misalin karfe 5:15 yayinda ake Sallah ya tayar da Bam. Ya kashe mutane takwas tare jikkata wasu biyar.” Mutane bakwai suka mutu a take cikin masallacin yayinda daya ya cika a hanyar asibitin Maiduguri.” Wani mazaunin garin Umar Goni ya bayyana cewa yana hanyar zuwa masallacin ne Bam din ya tashi kuma ya taimaka wajen ceton mutane tare da jami'an CJTF.


DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com

Comments