BIRNIN GWARI: ‘YAN SANDA BIYU, MAHARA BIYU SU RASU
Kakakin
rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna Mukhtar Aliyu ya bayyana cewa rundunar ta
rasa jami’an ta biyu a batakashi da suka yi da wasu ‘yan bindiga a dajin
Birnin-Gwari zuwa Funtua.
Aliyu
ya ce maharan sun ya wa jami’an ‘yan sandan kwantar bauna ne suka far musu a
daidai suna sintiri a yankin.
Bayan
batakashi da aka yi da su wadannan maharan, wasu jami’ai biyu sun rasu sannan
an kashe mahara biyu.
Sai
dai kuma bayan an kwashi gawan ‘yan sandan zuwa Kaduna ne aka sake samun wani
hadarin inda bindigar wani jami’i ta tashi ba da sanin sa ba ta sami wata mata
a jiki. Maza-maza aka garzaya da ita asibiti sai dai Allah yayi mata cikawa
kafin a iya shayo kanta.
”
Muna matukar juyayin rasuwar wannan mata da hadarin bindiga ya sameta, duk da
cewa mun kai ta asibiti Allah bai yi za ta rayu ba.” Inji Aliyu.
Idan
ba a manta ba rundunar ‘yan sandan Najeriya ta saka naira miliyan 5 ga duk
wanda ya tona asirin wadanda suka kashe jami’an ‘ya sanda 5 a garin Abuja da
Edo.
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku