BELIN DASUKI: KOTU TA AIKA WA SSS DA MINISTAN SHARI’A SAMMACIN SU SAKI DASUKI

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta aika da sammacin a gaggauata sakin Sambo Dasuki. Ta aika sammacin ne ga Babban daraktan SSS da ake kira DSS da kuma Antoni Janar na Najeriya, Abubakar Malami.

A ranar Talata ne dai Dasuki ya cika sharuddan belin sa da kotun ta bayar tun a ranar 2 Ga Yuli.
Jaridar PRNigeria ta ruwaito cewa ran talata ne da misalin karfe daya na rana, mutane biyu da suka tsaya belin Dasuki tare da jami’in bada beli na kotu, suka dunguma suka kai wa SSS da kuma Ministan Shari’a sammacin sanarwar a saki Dasuki.
Duk da cewa masu karbar belin sun yi tsammanin cewa za a damka musu Dasuki, majiya ta ce sai Darakatan SSS ya nemi iznin sakin sa daga fadar shugaban kasa tukunna.
Sau takwas kotu na bada belin Dasuki, kuma sauk bakwai kotu na kin bada belin sa.
Tun ranar talata ‘yan uwa da abokan arzikin Dasuki suka cika gidan sa su na jiran isowar sa.




DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com


Comments