BABBAN MASHAWARCIN HON. DOGARA YA FICE DAGA APC
Mashawarcin Kakakin
Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara, a kan Ayyuka na Musamman, ya fice daga
jam’iyyar APC.
Usman Bawa, da aka
fi sani a Kaduna Shehu ABG, wanda ya taba yin dan majalisar Tarayya inda ya
wakilci Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa, ya fice daga APC ne a yau Litinin.
Ya aika da wasikar sanar da cewa ya fice daga
jam’iyyar ne a ranar 14 Ga Yuli, inda sakon ya isa ga Shugaban APC na Karamar
Hukumar Kaduna ta Arewa.
Bawa ya fara aiki tare da Dogara a cikin 2015, tun
bayan da aka nada shi kakakin majalisa.
Kakakin yada labaran Dogara, Turaki Hassan ya
tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa.
Duk da dai bai fadi dalilin barin sa jam’iyyar ba,
ya bayyana cewa zai yi gaba ne domin ya gusa daga inda ya ke.
Har yanzu dai bai ce ga jam’iyyar da ya tuma tsalle
ya dirga a ciki ba.
Dama kuma cikin watan Yuni ne Hakeem Baba-Ahmed daga
Kaduna shima ya fice daga APC.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com

Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku