APC TA LASHE ZABEN JIHAR EKITI
Ba kamar yadda mutane musamman ‘yan
siyasa suke tunani ba cewa Fayose zai taka rawar gani a zaben jihar Ekiti da ya
gudana wajen tabbatar da ko ta halin kaka sai dan takarar jam’iyyar sa ta PDP
ya lashe zaben gwamnan jihar.
Abin dai ya zama tarihi yanzu domin
kuwa an gwada karfi tsakani jam’iyyun biyu a jihar sannan ‘yan takarar biyu duk
sun fafata, sai dai kash sakamakon zaben ya ba da PDP domin kuwa cikin kananan
hukumomi 16, APC ta lashe 12 ita kuma PDP ta cinye sauran hudun.
Idan ba a manta ba tun a shekarar
2016 tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose ya ke kurin wai shi cikakken dan
tasha ne, wanda gaba daya babu sako ko lungun da bai sani ba a jihar Ekiti,
sannan kuma bashi da wata sana’a da wuce siyasa.
” Allah ya kai mu 2018, zan nuna wa
Fayemi na APC cewa shi ba dan tasha ba ne. Nine a garin Ekiti kuma bani da
sana’ar da ta wuce siyasa. Yadda kasan Dutse haka nike, ka dake ni ka karairaye
in dake ka ka rugurguje. Haka zan yi wa APC.” Inji Fayose Kafin Zabe
Sai dai kuma duk da cika bakin da
yayi sai gashi ko karamar hukumar sa ya kasa ci.
Bayan haka jam’iyyar PDP ta ce tana
ganawa a tsakanin mambobin ta sannan za ta fitar da matsayar ta game da
sakamakon Zaben.
APC ta lashe zaben da Kuri’u 197,459
daga kananan hukumomi 12 da ya lashe ita kuma PDP ta samu kuri’u 178,121.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya
mika sakon taya Fayemi murnar lashe zaben da yayi sannan ya jinjina wa hukumar
zabe gane da yadda ta suka gudanar da zaben a jihar.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku