AMBALIYA TA CI RAYUKA 44 ‘A KATSINA
Gwamnan Jihar
Katsina, Aminu Masari, ya bayyana cewa ambaliyar da ta afku a Karamar Hukumar
Jibiya, ta ci rayuka 44, yayin da har yanzu ana neman wasu mutane 20 ba a kai
ga gano su ba.
Masari ya bayyana
haka ne a yammacin Litini bayan ya kai ziyarar jaje a yankin da ambaliyar ta
afku.
Ya kara da cewa an yi asarar dabbobi masu yawa yayin
ambaliyar, wadda ta afku sakamakon ruwan da aka rika shekawa da daren Lahadi,
har sama da awa uku.
“Ni dai da ido na ban taba ganin irin wannan
mummunan bala’i ba.” Inji Masari a cikin jimami.
“Tsawon tashin ruwan sama da ya yi toroko, ya kai
kafa goma. Sai dai mu ce wannan ibtila’I ce daga Allah kawai, domin duk mun
gina magudanan ruwa da kai kwararar da ruwa a cikin Kogin Jibiya.
“Amma ruwan da ke malalawa cikin kogin ne ya rika
dawowa da baya zuwa cikin gari.
“Na ga matashi ango sabon aure, kwana uku da daura
aure, ya na ta fagamniyar neman amaryar sa. Abin ban-tausayi.
Tuni dai Masari ya ce an maida wadanda suka rasa
matsugunan su zuwa firamare ta garin, kuma NEMA ta kai agajin gaggawa na kayan
abinci da sauransu, har cikin mota 13.
Ya kuma yi kira ga Ma’aikatar Muhalli da a karkatar
da ruwan, ta yadda zai daina kwarara a cikin kogin.
Kafin zuwan gwamna Masari garin Jibiya, shugaban
hukumar NEMA na jihar Aminu Waziri ya sanar da afkuwar wannan ibtila’I da irin
gudunmuwar da hukumar ta kai wa mutanen na gaggawa.
Ya bayyana cewa wannan ambaliya a fadawa kauyukan
Tundun Takari, Dan Tudu, Unguwar Kwakwa da Unguwar Mai Kwari duk dake karamar
hukumar Jibiya din.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku