ALLAH YAYIWA TSOHON GWAMNAN GOMBE, HASHIDU RASUWA
Allah yayiwa tsohon gwamnan jihar Gombe, Abubakar Hashidu
rasuwa.
Wata majiya tace Hashidu ya rasu a safiyar ranar Juma’a, 27
ga watan Yuli a gidansa dake Gombe bayan fama da rashin lafiya na tsawon wasu
shekaru. Ya kuma rasu yana da shekaru 74 a duniya. Mista Hashidu ya yi gwamnan
jihar Gombe daga watan Mayu 1999 zuwa watan Mayu 2003. An zabe shi a karkashin
lemar jam’iyyar All Peoples Party (APP).
Wani makusancin iyalan marigayin ya
tabbatar da mutuwar tsohon gwamnan kuma za’a binne shi da karfe 5pm na yammacin
yau Juma’a.
Arigayin ya kuma rike mukamin ministan ruwa da kuma minitan
gonad a ci gaban karkara a lokacin mulkin Ibrahim Babangida.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com

Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku