SHUGABANNIN JAM'IYYAR APC 11 DA AKA ZABA BABU HAMAYYA TARE DA OSHIOMHOLE
Jam'iyyar APC ta tabbatar da tsohon shugaban kungiyar kwadago na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Edo, Kwamared Adams Oshiomole a matsayin sabon zababen shugaban ta na kasa
Mr Oshiomole ya yi nasarar zama sabon shugaban jam'iyyar ne
cikin sauki saboda dukkan sauran abokan takararsa sun janye. Kazalika haka
ragowar shugabannin jam'iyyar 11 aka zabe su ba tare da abokan hamayya ba, ta
hanyar yin sulhu tsakanin masu takarar kujeru daban-daban. Ga jerin sunayen su
da mukaman su;
1. Ibrahim Masari, - Sakataren walwala.
2. Tunde Bello, - Sakataren kudi.
3. Zakari Mohammed - Sakataren jam'iyya na yankin arewa ta
tsakiya.
4. Hassana Abdullahi, - Shugabar mata ta yankin arewa ta
tsakiya.
5. Nelson Abba, - Ex-officio na yankin arewa ta
tsakiya.
6. Abubabakr Ajiya, - Sakataren jam'iyya na yankin arewa
maso gabas.
7. Isa Azare, - Ex-officio na yankin arewa maso
gabas.
8. Tukur Gusau, - Sakataren jam'iyya na yankin arewa
maso yamma
9. Nasiru Haladu, - Ex-officio na yankin arewa maso yamma
10. Mrs Rachael - Akpabio, Shugabar mata ta yankin
arewa ta kudu maso kudu
11. Misbahu L Didi, - Wakilin masu bukata ta musamman
Da akwai yiwuwar ta hanyar sulhu za a fitar da ragowar
shugabannin jam'iyyar 42 kamar yadda aka sanar da wadannan ya zuwa yanzu.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta
Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku