RIKICIN MAKIYAYA DA MANOMA: OBASANJO YA KAI ZIYARAR JAJANTAWA GARIN JOS
Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya yi kira ga
gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta tabbatar da cikakken binciken
kwakwaf don gano masu hannu cikin kisan kiyashi da aka yi ma jama’a a jihar
Filato, inji rahoton gidan talabijin na Channels.
Obasanjo ya yi wannan kira ne a ranar Laraba, 27 ga watan
Yuni yayin wata ziyarar jaje da ya kai jihar, inda ya samu ganawa da gwamnan
jihar, Simon Lalong, kamar yadda majiyar NAIJ ta ruwaito.
A cewar Obasanjo, kamata ya yi a gano musabbabin dake haddasa
rikicin, don shawo kansa tare da kare kara faruwar hakan a gaba; “Mu gano
gaskiyan abinda ke janyo wannan rikici, dole ne akwai abinda ke haddasawa.
“Idan har bamu yi haka ba, tabbas za’a cigaba da zubar da jinni babu gaira babu
dalili, don haka ya zama wajibi mu magance musabbabin wadannan rikita rikita,
saboda mun sani duk wata matsala tana da hanyar maganceta.” Inji shi. Obasanjo
ya kara da cewa a yayin da ake gudanar da wannan bincike, ya dace gwamnatin
tarayya ta hada kai da gwamnatin jihar Filato da kananan hukumomin da abin ya
shafa, har ma da shuwagabannin al’ummomin yankin.
Dayake nasa jawabin, gwamna Simon Lalong ya bayyan rikicin a
matsayin abin takaici, inda yace zaman lafiya fi zama dan Sarki, don kuwa idan
akwai zaman lafiya a jihar Filato, tabbas duk dan kirki zai ji dadi.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku