RASHIN ADALCI NE A CE NA YI SHIRU KAN KASHE-KASHEN MAKIYAYA - BUHARI
A ranar Talatar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu
Buhari, ya kalubalanci masu zargin sa da cewar ya sanya idanu kurum kan
kashe-kashen da makiyaya ke faman aiwatar wa cikin wasu sassa na kasar nan.
Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, shugaba
Buhari ya bayyana cewa masu gudanar da wannan zargi da tuhuma a kansa ba su
aikata daidai tare da rashin adalci a gare sa. Cikin jawaban kakakin shugaban
kasa, Mallam Garba Shehu ya bayyana cewa, shugaba Buhari ya yi wannan furuci ne
yayin taron ganawa da masu ruwa da tsaki a birnin Jos na jihar Filato dangane
da harin da ya afku cikin jihar a kwana-kwanan nan da ya salwantar da rayukan
mutane da dama. Shugaba Buhari yake cewa, watakila wasu al'ummar kasar nan na
zargin sa da nuna halin ko in kula dangane da rikicin makiyaya sakamakon
kamanceceniya da yake da ita irin tasu. sauran 'yan tawagar shugaban kasar sun
hadar da; Ministan tsaro Mansur Dan-Ali, Ministan harkokin cikin gida
Abdurrahman Danbazau da kuma Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Muhammad.
Tawagar ta shugaba Buhar ta kuma hadar da; Shugaban hafsin
sojin sama na kasa, Air Vice Marshall Sadique Abubakar da kuma sufeto janar na
'yan sanda, Ibrahim K. Idris. Sauran jiga-jigan masu ruwa da tsaki da suka
halarci taron ganawa da shugaba Buhari sun hadar da; Ma'aikatan Majalisun
dokoki na jiha da na tarayya, Sarakunan Gargajiya da kuma shugabannin kungiyar
Kirista ta Najeriya watau CAN da kungiyar Jama'atu Nasril Islam.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta
Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku