MAKIYAYA SUN KAI WANI MUMMUNAR HARI A JIHAR ADAMAWA
Kamar yadda kafar watsa labarai ta Channels TV ta ruwaito mun samu rahoton cewa, akalla rayuka 18 ne suka salwanta tare da jikkatar da dama a sanadiyar wani harin da ya afku a kayuen Dowayan dake karamar hukumar Demsa ta jihar Adamawa.
Makwabta wannan yanki da suka ziyarci kauyen sun shadaiwa manema labarai a ranar Asabar ta yau da cewa, ana zargin Makiyaya da kai wannan hari a daren ranar Juma'ar da ta gabata.
Mazauna kauyen na Dowayan sun bayyana cewa, makiyayan sun gudanar da wannan harin ne da misalin karfe 8.00 na daren ranar Juma'ar da ta gabata inda suka kone gidaje da dama da kuma dukiyar al'umma.
Mun fahimci cewa, a baya Makiyaya sun kai hari kan kananan hukumomin Numan, Demsa da Gerei dake jihar ta Adamawa.
Sai dai a yayin tuntubar Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, Othman Abubakar ya bayyana cewa, har yanzu bai samu wani rahoton dangane da wannan hari ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta
Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku