KOTU TA KORI KARAR NEMAN TSIGE GWAMNAN JIHAR KEBBI
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta kori
karar da aka gabatar a gaban ta, wadda aka kalubalanci sahihancin cancantar
Gwamna Abubakar Bagudu zama gwamnan jihar Kebbi.
Bagudu ya
samu kalubalanta a matsayin sa na dan takarar gwamna a karkashin APC, daga dan takarar
PDP, Sarkin Yaki, wanda ya nemi kotu ta soke satifiket din da aka ba Bagudu, a
matsayin wanda ya ci zabe, domin a cewar Sarkin Yaki, bai cancanta ba.
Sarkin
Yaki ya zargi Bagudu da kantara wa Hukumar ZABE Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC)
karya, don haka ya ce ya kamata kotu ta haramta zaben sa da aka yi.
Sai di
kuma Mai Shari’a na Babbar Kotun Tarayya a Abuja, Ahmed Mohammed, ya ce mai
karar ya kasa gabatar wa kotu kwararan shaidun da za su tabbatar wa kotu cewa
Bagudu ya kantara karya.
Dailin
haka ne ya kori karar saboda rashin sahihan shaidu.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta
Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku