HARIN FILATO: BA MU CE RAMUWAR GAYYA AKA YI BA, KAZAFI A AKA YI MANA – MIYETTI ALLAH
Shugaban Miyetti Allah na yankin
Arewa Maso Tsakiya Danlaci Ciroma ya yayi suka da kakkausar murya game da yadda
wasu gidajen jaridu a kasar nan suka yi ta yayada cewa wai harin da aka kai wa
mazauna kauyukan jihar Filato ramuwar gayya ce na kisan da akayi wa makiyaya.
Ciroma
ya ce wannan magana bai taba yin ta ba sannan bai san da ita ba kamar yadda aka
yi da yadawa a kafafen yada labarai. Ya ce bai yi hira da wani gidan jarida ba
saboda haka bai san inda suka samo wannan magana.
A
bincike da muka gudanar game da haka ashe wani dan jarida ne ya kissa wannan
magana cewa wai shi Ciroma ya fadi haka inda ya aika wa ‘yan uwansa manema
labarai ta shafin guruf din su a WhatsApp.
Daga
nan kuma sai suka yada ta ganin cewa shi wannan dan uwa nasu dan jarida ne ya
tabbatar musu da samun wannan magana na Ciroma baki-da-baki.
Amma
sai dai bayan binciken da aka gudanar, sai aka gane cewa tabbas, akwai gashi a
cikin maganar, aka gano cewa Ciroma bai taba yin irin wannan magana ba.
A
haka dai har da mu da muka dauki labarin kuma muka
gudanar da binciken muke janye wannan magana sannan muke rokon yafiya ga
kungiyar Miyetti. dauka mukayi a jaridar Nation.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta
Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku